Ministan ya ce, kungiyar IS suna amfani da kowane irin makami ne domin kisan gilla kan al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba, don haka ne ma ya nemi kwamitin MDD da ya tallafawa sojojin Libya da makamai domin kawar da mayakan na IS da masu taimaka musu.
A makon jiya ma fada ya barke tsakanin mayakan na IS da dakarun kasar Libya bayan kashe wani fitaccen malamin salafiyya a birni mafi girma dake karkashin ikon kungiyar ta IS wanda ke da nisan kilomita 500 daga birnin Tripoli.
Wata majiya daga hukumomin kasar ta ce, a kalla mutane 15 ne rikicin ya rutsa da su.
Tawagar ba da tallafi karkashin ikon MDD dake kasar Libya ta yi Allah wadai da hare haren kungiyar ta IS a yankin Sirte tare da hallaka mutanen da ta yi garkuwa da su tun watan Mayu.
MDD ta ce, samar da maslaha tsakanin jam'iyyun siyasar Libya da ba sa ga maciji da juna zai taimaka wajen fuskantar hanyoyin da za'a fatattaki mayakan kungiyar ta IS. (Ahmad Fagam)