Mambobin kwamitin tsaro sun bukaci dukkan bangarorin Libiya da su amince da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar siyasa da aka gabatar a ranar 8 ga watan Oktoba da kuma dukufa wajen kafa gwamnatin hadaka, a cikin wata sanarwar da kwamitin ya fitar a cibiyar MDD dake birnin New York.
A cikin sanarwar, mambobin kwamitin tsaron sun jaddada cewa yarjejeniyar wani muhimmin hange ne na hanyoyin warware rikicin siyasa, tsaro da tsarin doka da oda a Libiya.
A cikin wannan sanarwa, kasashe mambobi goma sha biyar na kwamitin tsaro sun jaddada niyyarsu game da yancin kai, 'yancin fadin kasa da kuma hadin kan 'yan kasa na Libiya.
Hakan ma cikin watan Oktoba, sakatare janar na MDD Ban ki-moon ya gayyaci mahalarta a taron tattaunawar siyasa na Libiya da su cimma cikin gaggawa shirin da kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da zata kai ga kafa wata sabuwar gwamnati.
Libiya, kasa ce mai arzikin man fetur dake arewacin Afrika, da kuma take fama da rikicin siyasa tun bayan kifar da tsohon shugaban kasar Mouammar Kadhafi a shekarar 2011. (Maman Ada)