in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libiya ta yi watsi da tande tanaden yarjejeniyar zaman lafiya ta MDD
2015-09-16 13:33:11 cri
Majalisar dokokin kasar Libya da gamayyar kasa da kasa ta amince da ita ta yi watsi da wasu sabbin tanade tanaden yarjejeniyar zaman lafiya da MDD ta gabatar.

Wata sanarwa da wakilan suka gabatar ta bayyana cewa, zauren wakilan ya yi watsi da dukkan tanade tanaden dake cikin wannan yarjejeniyar farko da aka sanya wa hannun a baya bayan nan.

Majalisar dokokin ta kuma sanarwar da cewa, za ta janye tawagarta da ta tura kasar Morroco, don tattauna harkokin siyasar kasar a karkashin jagorancin MDD.

Majalisar ta jaddada cewa, za ta cigaba da aiki har zuwa karshen wa'adinta kuma za ta fara aiwatar da jadawalin da aka tsara na tabbatar da mika mulki cikin lumana kamar yadda doka ta tanada.

Tun a watannin da suka gabata ne tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD (MANUL) da ke aiki a kasar ta Libya, ta dauki nauyin shirya wasu jerin tarukan shawarwari na siyasa tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a kasar, da zummar kawo karshen rikicin kasar.

Bernardino Leon, manzon musammun na sakatare janar na MDD kana shugaban tawagar ta MDD da ke kasar Libya, ya bayyana a ranar Lahadi cewa bangarorin da ke gaba da juna a kasar Libiya sun kai ga cimma daidaito kan wasu muhimman batutuwa game da yarjejeniyar siyasar kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China