in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin Libya sun kulla yarjejeniyar siyasa
2015-12-18 10:19:58 cri
Wakilan majalissun dokokin biyu dake adawa da juna na kasar Libya, da wasu wakilan dake halartar shawarwarin siyasar kasar, sun kulla yarjejeniyar siyasa a birnin Skhirat na kasar Morocco.

A jiya Alhamis ne tawagar musamman da MDD ta tura zuwa kasar Libiya ta jagoranci aikin kulla yarjejeniyar. A yayin taron, wakilin musamman na MDD kan batun Libya, kana shugaban tawagar Martin Kobler, ya bayyana cewa wannan rana ta kasance wata muhimmiyar rana a tarihin kasar Libya, kuma kulla yarjejeniyar ta zamo matakin farko na dawo da Libiyan kan turba ta samun ci gaban kasa.

Kaza kila, bisa yarjejeniyar, kwamitin firaminista dake kunshi da wakilai 9 da aka kafa yayin shawarwarin siyasar kasar, zai dauki alhakin gudanarwar ayyukan sabuwar gwamnatin hadin kan al'ummomin kasar, sa'an nan, majalisar wakilan jama'ar kasar Libya da aka kafa bisa amincewar gamayyar kasa da kasa, za ta kasance hukumar kafa dokokin kasar.

Daga bisani kuma, za a kafa wani kwamiti na musamman domin ba da shawara ga sabuwar gwamnatin. Bugu da kari, kwamitin firaminista mai wakilai 9 zai gabatar da jerin sunayen ministocin sabuwar gwamnatin kasar cikin wata guda, sa'an nan kwamitin sulhun MDD zai duba jerin sunayen kafin a amince da shi.

Har wa yau, yarjejeniyar ta nuna cewa, ya kamata sabuwar gwamnati ta fara gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci, da yin kwaskwarima, da kafa sabbin hukumomin gwamnati, da farfado da tattalin arzikin kasa ba tare da bata lokaci ba.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China