Bayan Faiz Saraj da zai kasance firaminista, takardar sunayen masu bada shawara ga shugaban kasa na kunshe da mambobin shida da suka hada da Ahmed Maiteeq, Fathi Majibri, Moussa Al Kouni, mataimakan faraminista uku, da kuma Muhammad Ammari da Omar Al Aswad, wasu manyan ministoci biyu, in ji mista Leon.
A cewar manzon, muhimman bangarorin siyasa biyu na Libiya, wato majalisar wakilan Libiya dake Tobrouk da kuma babban zauren kasar Libiya (CNG) dake Tripoli, dole ne su cimma wata yarjejeniyar sulhu kan takardar sunayen masu bada shawara ga shugaban kasa nan da karshen wannan mako.
Mista Leon ya koma tattaunawa a ranar Talata a Skhirat tare da bangarorin Libiya domin cimma wata yarjejeniyar karshe da za ta gamsar da kowa kan rikicin Libiya.
Birnin Skhirat na Morocco ya karbi a cikin watan julin da ya gabata, da taron rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin bangarori daban daban na Libiya da suka halarci taron, da suka hada da shugabannin jam'iyyun siyasa wadanda suka halarci taruka makamantan haka har sau shida a karkashin jagorancin MDD, amma ba tare da samun halartar wakilan CNG ba. (Maman Ada)