Taron kolin shi ne babban taro na farko da aka kira a yankin Turai da ya hada da manyan shuwagabanni da jami'an gwamnatocin kasashen Turai, bayan harin ta'addancin da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa kusan makonni biyu da suka gabata. Taron na kwanaki uku mai taken "kyautata tasirin kasa da kasa" ana sa ran tattauna yadda za a iya fuskantar sauyin yanayi da kuma yaki da 'yan ta'adda.
An haifi Patricia Scotland mai shekaru 60 a kasar Dominica, wadda ta taba yin aikin babbar mai gabatar da kara a kotun England, Welsh da kuma Arewacin Ireland. A yayin taron da aka yi a wannan rana, madam Scotland ta lashe zaben babban sakataren kungiyar Commonwealth cikin takarar da ta yi da wassu guda biyu, lamarin da ya sa, aka samu mace ta farko da za ta rike matsayin babbar sakatariyar kungiyar Commonwealth. Madam Scotland za ta fara aikinta a hukunce a ranar 1 ga watan Afrilu na shekarar 2016, bayan babban sakataren kungiyar na yanzu Kamalesh Sharma ya kammala wa'adin aikinsa. (Maryam)