in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kasashen renon Ingila ya cimma matsaya kan batun sauyin yanayi
2015-11-30 09:48:05 cri

Taron karawa juna sani na shugabannin kasashen renon Ingila CHOGM, wanda aka kammala a ranar Lahadin nan a Malta, ya cimma matsaya kan sabbin matakan da za'a dauka domin tunkarar matsalar sauyin yanayi.

Taron na kwanaki 3 mai taken karawa duniya armashi, ya samu halartar shugabanni daga kasashen renon Ingila 53, sannan sun hada da shugabannin kasashe 31.

Taron ya gudana a daidai lokacin babban taron MDD kan sauyin yanayi a Paris, babban sakataren MDD Ban Ki-moon da shugaban kasar Faransa Francois Hollande sun bi sahun shugabannin kasashen a yayin gudanar da taron kan batun sauyin yanayi.

Sanarwar bayan taron na CHOGM, ta nuna cewar, shugaabannin kasashen renon Ingila sun amince da yin aiki tare don tunkarar matsalar sauyin yanayin, kamar yadda taron MDD kan sauyin yanayin UNFCCC ya gudana a birnin Paris.

Bugu da kari, taron ya yi magana da murya guda, wajen yakar ayyukan 'yan tada kayar baya da masu kaifin kishin addini.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China