Babban wakilin Sin mai halartar shawarwarin Su Wei ya yi bayani cewa, an yi shawarwarin yadda ya kamata, inda bangarori daban daban suka duba tare da takaita takardar Geneva da bayyana matsayin su, wanda ya aza tubali ga gudanar da shawarwari na zagaye na uku a watan Agusta na bana. Kana bangarori daban daban sun kara amincewa da juna a gun shawarwarin.
Hakazalika kuma, Su Wei ya bayyana cewa, Sin za ta shiga shawarwari kan yanayi na duniya, da yin mu'amala tare da bangarori daban daban, da sa kaimi ga cimma nasara a taron yanayi a birnin Paris, da bada jagoranci wajen gudanar da ayyuka ba tare da gurbata yanayi ba da kuma samun bunkasuwa mai dorewa. (Zainab)