A yayin taron manema labaran da aka kira a birnin Mellieha na kasar Malta, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, za a kira taron masu kulla yarjejeniyar sauyin yanayi na MDD karo na 21, watau babban taron sauyin yanayi na Paris tun ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa ranar 11 ga watan Disamba a birnin Paris, inda ake fatan bangarorin da abin ya shafa za su iya kulla yarjejeniyar mai amfani a birnin Paris.
Ban Ki-moon ya kuma ambaci sanarwar sauyin yanayi da shugabannin Sin da Faransa suka samar cikin hadin gwiwa a ranar 2 ga watan Nuwamba a birnin Beijing, inda ya ce, kasar Sin da kasar Faransa sun yi alkawari cikin sanarwar cewa, za su gudanar da bincike kan yadda aka cimma burin da kuma ci gaba da aka samu kan aikin cikin ko wane shekaru biyar bisa dukkanin fannonin da abin ya shafa, lamarin da ya samu goyon baya daga galibin mambobin kasashen MDD. (Maryam)