Farhan Haq, mataimakin kakakin Ban Ki-moon ya yi tsokaci a yayin taron manema labaru, cewar kasashen Sin da Koriya ta Kudu sun gabatar da jerin matakan da za su dauka wajen magance matsalar sauyin yanayi a wancan rana, wanda ya sa kaimi da kuma bayar da gudummawa ga yadda za a cimma daidaito kan sabuwar yarjejeniya game da sauyin yanayi a yayin babban taron yanayi na Paris da za a kira a karshen bana.
Mr. Haq ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu dai kasashe sama da 40 sun riga sun gabatar da matakansu kan magance matsalar sauyin yanayi, wadanda za su shafi kashi 60 cikin dari na yawan iska masu gurbata muhalli da ake fitarwa a duk duniya.(Kande Gao)