in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabunta: Ana samun ci gaba a shawarwari kan cimma sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi ta duniya
2015-06-12 18:57:44 cri

An rufe shawarwari na zagaye na biyu na MDD game da sauyin yanayi na shekarar 2015 a birnin Bonn dake kasar Jamus a jiya Alhamis 11 ga wata. Masu halartar shawarwarin da masu kallo sun bayyana cewa, ana samun ci gaba a shawarwari kan cimma sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi ta duniya, wanda ya aza tubulin sa kaimi ga cimma sabuwar yarjejeniyar a gun taron yanayi da za a gudanar a birnin Paris a karshen bana.

Babban wakilin Sin mai halartar shawarwarin Su Wei ya yi bayani cewa, an yi shawarwarin yadda ya kamata, inda bangarori daban daban suka duba tare da takaita takardar Geneva da bayyana matsayin su, wanda ya aza tubali ga gudanar da shawarwari na zagaye na uku a watan Agusta na bana. Kana bangarori daban daban sun kara amincewa da juna a gun shawarwarin.

Hakazalika kuma, Su Wei ya bayyana cewa, Sin za ta shiga shawarwari kan yanayi na duniya, da yin mu'amala tare da bangarori daban daban, da sa kaimi ga cimma nasara a taron yanayi a birnin Paris, da bada jagoranci wajen gudanar da ayyuka ba tare da gurbata yanayi ba da kuma samun bunkasuwa mai dorewa.

Bugu da kari, Su Wei ya ce, kasar Sin na kokarin gabatar da shirin ba da karin gudummawa kan fuskantar sauyin yanayi bayan shekarar 2020 a hukunce cikin watannin 6 na farkon wannan shekarar, wanda zai kasance cikin sabbin gudummawa da kasar za ta samar wajen fuskantar sauyin yanayin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China