Wani rahoton bincike da kungiyoyi masu zaman kansu 18 suka fitar a ranar Litinin, ya nuna cewar, har yanzu kasashen da suka ci gaba ba su bayar da kasonsu ba na yaki da matsalar sauyin yanayi.
Idan aka yi la'akari da irin bukatar da aka gabatar a lokacin taron kasashen duniya kan matsalar dumamar yanayi a birnin Bonn na kasar Jamus gabaninin gudanar da taron a birnin Paris, manyan kasashen duniya sun yi alkawarin daukar matakan rage dumamar yanayi, ba ma ga daukar mataki na kashin kai ba, a'a har ma da alkawarin ba da tallafin kudade don tunkarar shirin rage matsalar.
Sama da kasashen duniya 150 ne suka gabatar da shirinsu na tunkarar matsalar sauyin yanayi wato INDC ga MDD, gabannin gudanar da taron, wanda ake sa ran gudanarwa a watan Disamba a birinin Paris, taron zai mai da hankali kan nazarin kashi 90 na sinadarin Carbon a duniya.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewar, rashin daukar matakan da suka dace wajen yaki da matsalar sauyin yanayi zai iya dagula al'amurra.
Kasar Amurka da EU sun gabatar da kashi 1 bisa 5 na shirin INDC, yayin da kasar Japan kadai za ta dauki ninki 10 na alkawari kan shirin tunkarar matsalar yanayin.(Ahmad Fagam)