A gobe ne wakilan Rasha, Amurka, MDD za su tattauna batun kasar Sham, inda ake fatan yayin taron MDD za ta jaddada wajibcin yaki da ta'addanci tare da yin kira ga bangarori daban-daban da su kara hadin gwiwa tsakaninsu a yakin da ake yi da ta'addanci.
Ban da wannan kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a wani taron manema labaru a nan birnin Beijing yau cewa, yaki da ta'addanci wani muhimmin mataki ne wajen magance rikicin Sham.
Kasar Sin tana goyon bayan kasashen duniya da su hada kai kana su sulhunta a tsakaninsu kamar yadda ka'idojin MDD da dokokin kasa da kasa suka tanada, don yaki da ta'addanci, ta yadda za a samu nasarar kawar da ayyukan ta'addanci. Yanzu haka, ana kokarin gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen da batun Sham ya shafa karo na uku, kuma Sin tana fatan hadin gwiwar kasashe daban daban zai taimakawa wajen hanzarta warware batun Sham a siyasance. (Amina)