A cikin watan jiya, hukumar ta kuma yi yunkurin kafa ofishin shi a cibiyar MDD dake birnin New York da kuma Haque na kasar Netherlands, sannan kuma da wani a birnin Damascus na kasar Syria, in ji Mr. Haq a lokacin ganawar da ya yi da manema labarai a wannan rana.
Ya yi bayanin cewa hukumar ta hadin gwiwwa a yanzu yana da isassun ma'aikata da zai iya cewa ya fara aiki yadda ya kamata da wannan rana.
Babban sakataren kwamitin tsaron Majalissar ya aike da wasika dangane da hakan a ranar 10 ga wannan watan na Nuwamba. (Fatimah Jibril)