Gabanin bude taron na Saudiya, manyan 'yan adawar kasar sun bayyana aniyarsu ta halartar taron sasantawan, wanda ake fatan zai samu halartar jami'an diflomasiya na kasashen ketare ciki har da na kasar Rasha.
Kungiyar kawance ta Syria wato SNC a takaice, ta ce za ta yi amfani da wannan dama wajen hada kan dakarun 'yan adawa a kokarin da ake na kafa gwamnatin hadaka bisa tsarin yarjejeniyar da aka cimma tun farko a birnin Geneva.
Rahotanni na cewa, sama da wakilai 100 ke halartar taron da ministan harkokin wajen kasar ta Saudiya ya bude. (Ibrahim Yaya)