Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya ce kasarsa za ta ci gaba da hadin gwiwa da kasar Sham ta fuskar bunkasa dabarun aikin soja, domin cimma nasarar yakin da kasar ke yi da ayyukan ta'addanci.
Mr. Lavrov ya kuma jaddada cewa, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS babbar matsala ce da duniya ke fuskanta. Sai dai duk da hakan sojojin gwamnatin kasar Sham na kokarin sauke nauyin dake wuyansa na tinkarar kalubalen kungiyar ta IS, wadanda hakan ya zamo muhimmin karfi game da yakin da ake yi da kungiyar.
Ya ce kawancen dakile IS karkashin kasar Amurka zai samu ci gaba, muddin aka kara hadin kai da sojojin gwamnatin kasar Sham. Ban da haka kuma Mista Lavrov ya ce, baya ga baiwa kasar Sham makamai, abin da ya zama wajibi ga Rasha shi ne ta tura masananta ta fuskar kimiyyar soja zuwa kasar, da zummar koyar da sojojin kasar dabarun amfani da makamai na zamani.
Wasu kafofin yada labarai na kasar Amurka sun labarta cewa, Rasha na shirin gudanar da babban aikin soja a Sham. Game da hakan, a kwanakin baya kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, Sham ta yi alkawarin amfani da makaman da ta saya daga Rasha wajen yaki da ta'ddanci, kuma kasar ta Rasha na fatan taimakawa Sham din a wannan fanni. (Amina)