Haka kuma, Sergei Lavrov ya bayyana a wannan rana cewa, bisa goyon bayan da sojojin saman kasar Rasha suke baiwa kasar Syria, gwamnatin Syria ta karfafa mulkinta a kasar, sojojin gwamnatin kuma sun cimma wasu nasarori kan matakan soja da suka dauka, kaza kila, kasar Rasha na da imani cewa, lamarin zai taimaka wa gwamnatin kasar Syria wajen aiwatar da yunkurin siyasa nata. A halin yanzu kuma, ya kamata kasar Syria ta fara shiryawa kan gudanar da babban zaben shugaban kasar da kuma zaben majalisar dokokin kasa.
Bugu da kari, Sergei Lavrov ya gaskata cewa, cikin shawarwarin da aka yi tsakanin shugabannin kasashen Rasha da Syria a ran 20 ga wata, bangarorin biyu sun yi shawarwari kan yunkurin siyasa na kasar Syria. Haka kuma, shugaban kasar Syria Bashar al-Assad yana ganin cewa, ban da daukar matakan soja kan 'yan ta'addan kasar, ya kamata a kuma yi hadin gwiwa da magoyon bayan gwamnatin kasar, domin aiwatar da yunkurin siyasa a kasar yadda ya kamata.
Daga bisani kuma, bisa labarin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fidda a ran 24 ga wata, an ce, Sergei Lavrov ya kuma tattauna tare da takwarorin aikinsa na kasar Amurka, kasar Iran da na kasar Masar ta wayar tarho, kan yunkurin siyasar kasar Syria. (Maryam)