Ma'aikatar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, hare-haren da Amurka suna mayar da hannun agogo baya ne a kokarin da ake na yaki da 'yan ta'adda.
Ma'aikatar ta ce, jiragen yakin kawance 4 ne suka kai hari da makamai masu linzami guda 9 kan sansanonin sojojin Syria da ke Deir al-Zour a lokacin da sojojin Syria ke fafatawa da kungiyoyin 'yan ta'adda a sassan kasar, inda suka halaka sojoji uku kana 14 suka jikkata.
Bugu da kari, hare-haren sun lalata motoci masu sulke guda 3, motocin daukar kayan yaki guda 4 da wasu manyan bindigogi.
Sanarwar ta ce, hare-haren kan sojojin da aka kai wata barazana ce ga zaman lafiyar shiyyar da ma duniya baki daya.
Don haka, ma'aikatar take kira ga kasashen duniya, da su yi Allah-wadai da wannan harin da ta ce ya saba dokokin MDD.
Wannan dai shi ne karon farko da kawancen da Amurka ke jagoranta ya kai hari kan wuraren da sojojin Syria suka ja daga, tun lokacin da suka fara kai hare-hare ta sama a kasar ta Syria sama da shekara guda da ta gabata. (Ibrahim)