Mr. Li har ila yau ya gabatar da ra'ayin gwamnatin kasar Sin game da daidaita batun Sham a siyasance bisa matakai hudu, wato da farko dai, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su tsagaita bude wuta da kawo karshen nuna karfin tuwo, kuma su yi alkawarin tinkarar ta'addanci. Na biyu, ya ce bisa shugabancin MDD, bangarori daban daban na Sham su amince da juna, kuma su yi shawarwari daga dukkan fannoni cikin adalci don su fitar da jadawalin daidaita harkokin siyasa ta wucin gadi bisa sanarwar Geneva. Babban jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, ya kamata a kaddamar da aikin sake bunkasa kasar Sham bayan yaki, ta yadda bangarori daban daban na Sham za su iya ganin makomar zaman lafiya. (Sanusi Chen)