in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha da Amurka sun yi shawarwarin tsaro game da ayyukan hare hare ta sama a Syria
2015-10-11 13:36:31 cri
Manyan jami'an tsaron Amurka da na Rasha sun gudanar da wata tattaunawa ta bidiyo kan batun tsaro a yayin da suke gudanar ayyukan kai hare hare ta sama a Syria, in ji Pentagone.

Tattaunawar ta kwararrun harkokin soja ta maida hankali musammun ma kan aiwatar da ayyukan tsaro na hakika, in ji Pentagone. An samu nasarori a yayin wannan tattaunawar bidiyo ta tsawon mintoci 90, in ji Pentagone, tare da kara cewa Amurka ta amince ta gudanar da wata tattaunawa tare da Rasha nan da dan lokaci mai zuwa.

Wannan tattaunawa ta baya baya ta zo kwanaki tara bayan wata tattuanawa ta farko tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu.

Wadannan shawarwari sun maida hankali kan warware sabanin da kasashen biyu suke da shi a Syria, musammun ma kan musanyar bayanai domin kaucewa hadura a sararin sama a yayin da bangarorin biyu suke gudanar da ayyukan kai hare hare ta sama kan kungiyar IS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China