Ministan harkokin wajen kasar ta Rasah Sergey Lavrov a jiya Alhamis ya kare aniyar kasar na harin bama bamai da take yi a Syrian, yana mai cewa, hakan an yi shi ne a kan 'yan ta'adda ba wai don a ci gaba da mara ma Shugaban kasar Bashar Al-Assad bayan ya ci gaba da mulki ba.
Ya ce suna ganin juna gaba da gaba tsakaninsu da sojojin Amurka da su ma suke harin kungiyar ISIL, Al-Nusra da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a lokacin da yake bayani a cibiyar MDD wanda ya ce suna da aniya iri daya.
A wani bangaren kuma hukumar tsaron Amurka ta Pentagon a ranar Alhamis din ta ce Amurkan da Rasha sun yi tattaunawar farko a game da harin sama da suke aiwatarwa a Syria.
Kakakin Pentagon Peter Cook ya ce tattaunawar na tsawon awa daya an maida hankali ne hanyoyin da za'a bi a aiwatar da harin cikin tsanaki ba tare da hadari ba.
Ya ce Amurka ta fara bayar da shawarari a inganta kai harin cikin tsanaki, a kiyaye lissafi bisa kuskure da kuma kauce ma daukan matakan karfi, ayyuka da tafiyar da duk wani abin da zai kawo zaman fargaba. (Fatimah Jibril)