Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Interfax ya bayar, an ce, lokacin da yake ganawa da manema labaru, Mr. Putin ya ce, ko da yake akwai babban gibin da ke kasancewa a tsakanin sharhohin kasashen Rasha da Amurka kan rikicin Sham, kasar Rasha tana kuma fatan kwararrun kasar Amurka wadanda suke shugabantar matakan yakar IS a kasar Sham za su iya nuna goyon bayan matakan dakile kungiyar IS da kasar Rasha take dauka. Putin ya bayyana cewa, masu tsatsauran ra'ayi na kasar Sham su barzana ne da kasar Rasha da kasashen yammacin duniya suke fuskanta tare, amma har yanzu kasashen yammacin duniya suna hakurinsu. Kafin kasar Rasha ta dauki matakan soja a kasar Sham, ta riga ta sanar wa kasar Amurka da kungiyar NATO wannan kuduri.
A ran 30 ga watan Satumba, bisa kudurin Putin, sojojin kasar Rasha sun fara kai hari daga sama kan dukkan sansanoni da kayayyakin kungiyar IS dake kasar Sham. (Sanusi Chen)