Shubannin biyu, sun yi wannan kiran ne yayin wani taro a jiya Jumma'a a birnin Paris, inda suka gargadi mista Putin da cewar ya tabbatar harin jiragen saman a Syria bai wuce iya maboyar 'ya'yan kungiyar ta IS ba.
Bayan kammala tattaunawa kan warware rikicin Ukraine da shugabannin suka gudanar, Merkel ta ce yanzu babban abin da ke gabansu shi ne ganin bayan kungiyar ta IS domin a cewarta a bayyane take abokan gaba ne, kuma yin galaba a kansu shi ne zai share fagen warware rikicin kasar Syria.
Da ma dai kafin gudanar da tattaunawa kan makomar Ukraine, shugaba Hollande ya yi wata ganawa da Shugaba Putin, kan yadda za'a tunkari shugaban Syria Bashir al-Assad domin kafa gwamnatin rikon kwarya da nufin warware rikicin siyasa a Syria. (Ahmad Fagam)