in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta yi bincike kan wadanda ke yin amfani da makamai masu guba a kasar Sham
2015-08-08 13:48:38 cri
A yayin taron kwamitin sulhu na MDD da aka yi a jiya 7 ga wata, an zartas da wani kuduri mai lamba 2235 na kafa hukumar bincike kan wadanda suke yin amfani da makamai masu guba a kasar Sham.

A yayin taron, Bashar Jaafari, wakilin dindindin na kasar Sham dake zaune a MDD ya bayyana cewa, a kullum gwamnatin kasar Sham na cika alkawuran na kaucewa amfani da makamai masu rai da na nukiliya da "yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba" da sauran kuduran kwamitin sulhu na MDD kamar yadda ya kamata. Sabili da haka, dakarun gwamnatin kasar Sham ba su taba, kuma ba za su yi amfani da makamai masu guba ba har abada. Malam Jaafari ya kuma zargi 'yan ta'adda dake kasar Sham da yin amfani da makamai masu guba.

Bayan da aka zartas da kudurin, Mr. Liu Jieyi, wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD ya bayyana cewa, bangaren Sin na maraba da wannan kuduri mai lamba 2235. Ko shakka babu bangaren Sin ya ki amincewa da yin amfani da makamai masu guba a kowane lokaci. Kuma bangaren Sin na goyon bayan MDD da ta daukin yin bincike cikin adalci kamar yadda ake fata, kuma yana fatan za a iya yanke hukunci ga wadanda suke amfani da makamai masu guba bisa laifuffukan da suka aikata. Bugu da kari, Mr. Liu Jieyi ya jaddada cewa, warware batun Sham a siyasance hanya daya tilo ce da ya kamata a bi wajen daidaita batun. Ya kamata gamayyar kasa da kasa ta tsaya tsayin daka kan matsayinta na daidaita batun Sham a siyasance, kuma ta goyi bayan MDD da ta taka rawa da bayar da gudummawarta wajen daidaita batun a siyasance.

Sannan bangaren Sin na fatan wannan kuduri mai lamba 2235 da aka zartas a yayin taron kwamitin sulhu na MDD zai bayar da gudummawa wajen dayanta ra'ayoyin kasashe mambobin kwamitin sulhu kan batun Sham, ta yadda za a iya samun sabon karfi na kokarin daidaita batun Sham a siyasance daga dukkan fannoni har abada kamar yadda ya kamata tun da wuri. Bangaren Sin zai ci gaba da taka rawarsa da ta dace ga wannan kokari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China