in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha za ta kara karfin dakile IS
2015-10-04 14:07:46 cri

Sojojin kasar Rasha sun ba da labari a ran 3 ga wata cewa, sojojinta na sama sun cimma nasarar dakile karfin kungiyar IS bayan matakin da suka dauka na kai hari ta sama. A cewarsu, za su kara himmatuwa wajen dakile kungiyar IS, kuma Rasha ta riga ta ba da shawara ga Amurka da ta janye sojojinta daga wasu wuraren da Rasha za ta kai wa hari tare da dakatar da zirga-zirga ta sararin saman kasar Sham. Firaministan Rasha Dmitri Medvedev ya shedawa manema labaru a wannan rana cewa, matakin soja da kasar Rasha ke dauka a Sham nada manufar kiyaye jama'ar Rasha daga barazana iri ta ta'addanci.

Ban da wannan kuma, shugaban hukumar bada jagoranci ta hedkwatar hafsan-hafsoshin dakarun kasar Rasha Mista Andrey Kartapolov ya bayyana a ran 3 ga wata cewa, Rasha ta tura jiragen sama sau 60, wadanda suka kai hare haren kan wuraren kungiyar IS fiye da 50 tun lokacin da ta fara kai hari ta sama a ranar 30 ga watan Satumba. Mista Andrey Kartapolov kuma ya ce, Rasha na fatan kara hadin gwiwa da kasashe daban-daban don dakile ta'addanci, kuma ta yi kira ga sauran kasashe da su samar wa juna bayanan da suke samu game da harkokin kungiyar a Sham da Iraqi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China