Mahalarta sun bayyana cewa, taron ya mai da hankali kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, matakin da zai fidda wata hanya mai haske ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu nan gaba, tare kuma da baiwa nahiyar Afrika taimako wajen raya tattalin arzikinta a fannoni daban-daban.
Shugaban kasar Kongo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 15 da suka gabata bayan kafuwar FOCAC, Sin da Afrika sun yi hadin gwiwa tsakaninsu da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kuma ka'idar kawo moriyar juna da amfanawa jama'ar bangarorin biyu. Taken taron da ake gudanarwa shi ne "Hadin gwiwa", wanda ke da ma'ana sosai, abin da kuma zai bayyana manyan fannonin da Afrika za ta mai da hankali wajen samun bunkasuwa nan gaba, da taimakawa nahiyar ta fuskar raya dangantaka a dukkanin fannoni. Haka kuma zai bada tallafi ga nahiyar wajen raya masana'antu, manyan ababen more rayuwa, aikin noma na zamani, sha'anin amfani da na'urori a fannin noma, zirga-zirga, ba da horo da ilmi.
A nasa bangaren, shugaban kasar Kongo Kinshasa, Joseph Kabila ya bayyana cewa, taron kolin Johannesburg na FOCAC zai samar da makoma mai kyau wajen raya dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin shekaru 15 masu zuwa. A yanzu nahiyar Afirka tana bunkasa lami lafiya, tare da kokarin kawar da talauci.
Mr Kabila ya ce daya daga cikin muhimman batutuwa na samun ci gaban Afirka shi ne yin hadin gwiwa da kasar Sin, a don haka ana fatan kara fadada kasuwannin Sin ga kayayyakin Afirka.
Shugaban kasar Habasha, Hailemariam Dessalegn a jawabinsa ya furta cewa, tsarin ziri daya da hanya daya da Sin ta fitar na da ma'ana sosai ga nahiyar Afirka, wanda ya bayyana karfin jagora na shugaban kasar Sin Xi Jinping. Ya ce Dandalin FOCAC ya ba da wani muhimmin dandali na karfafa dangantaka tsakanin kasashen Afirka da Sin. A gun liyafar da aka kira kafin bude taron, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, tattalin arzikin bangarorin biyu na iya taimakawa juna. A don haka Sin na fatan kara sa kaimi ga raya dangankata tsakaninta da kasashen Afirka. Haka ma a cewarsa, kasashen Afirka suke da wannan aniyar inganta hadin gwiwa da Sin a karkashin dandalin FOCAC.(Amina, Fatima)