in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin da Afirka abokai ne dake da buri iri daya
2015-12-04 16:13:02 cri
A yau Jumma'a 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a gun bikin bude taron koli na Johannesburg na FOCAC, inda ya jaddada cewa, tun asali Sin da Afirka abokai ne dake da buri iri daya. Suna da tarihi iri daya, da gwagwarmaya iri daya, shi ya sa akwai dankon zumunci tsakanin jama'ar bangarorin biyu.

Bayan haka, shugaba Xi ya bayyana cewa, tun asali Sin da kasashen Afirka suna taimakawa juna, inda ya yi misali da hanyar jirgin kasa dake hada da Tanzaniya da Zambiya da cibiyar taron kungiyar AU da Sin ta kafa a nahiyar Afirka, wadanda suka zama shaidar zumunci tsakanin bangarorin biyu. Bayan haka, a yayin kokarin shawo kan cutar Ebola, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun ba da taimako cikin yakini, sun ba da jagoranci ga kasashen duniya wajen ba da gudummawa ga nahiyar Afirka, hakan ya bayyana dankon zumunci dake tsakanin jama'ar Sin da ta kasashen Afirka.

Ya ce, kasashen Afirka sun goyi bayan kasar Sin wajen sake komawa teburin MDD ba tare da son kai ba, kuma sun ba da kudin agaji ga kasar Sin bayan abkuwar bala'in girgizar kasa na Wenchuan, da na Yushu da sauransu. Game da wadannan batutuwa, jama'ar Sin ba za su manta ba har abada.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China