An bude taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika(FOCAC) na tsawon kwanaki biyu a safiyar yau din nan Jumma'a 4 ga wata a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu. Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ya kasance cikin mahalarta taron a cikin jawabin da ya gabatar ya bayyana sabon ra'ayi, manufofi da matsayin da Sin ke dauka kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.
Mista Xi ya sanar da daga dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Don haka, ya yi kira ga Sin da kasashen Afrika da su tabbatar da ginshikai biyar dangane da dangantakar dake tsakaninsu, da amincewa da juna a siyasance, kawo moriyar juna a fannin tattalin arziki, kara mu'ammala ta fuskar al'adu, har ma da taimaka wa juna kan batun tsaro, da hadin gwiwa cikin harkokin kasa da kasa. (Amina)