in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron FOCAC ya jawo hankalin kafofin watsa labaru na Afirka
2015-12-04 15:47:02 cri
Taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC da za gudanar a birnin Johannesburg daga yau Jumma'a zuwa gobe Asabar 5 ga wata, da taron ministoci karo na 6 da taron tattaunawa kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, dukkansu sun jawo hankalin kafofin watsa labaru na Afirka.

Jaridar Cameroon Tribune ta bayar da labari a yau cewa, ministan harkokin wajen kasar Kamaru Lejeune Mbella ya yi nuni a gun taron dandalin ministocin cewa, Sin da Kamaru suna raya dangantakar abokantaka a fannoni daban daban kamar sufuri, samar da ruwa, makamashi, sadarwa, kiwon lafiya, harkokin wasanni, bada ilmi da dai sauransu.

Shi kuma ministan kula da harkokin tsare-tsaren yankunan kasar Louis Paul Motaze ya bayyana a gun taron cewa, daga shekarar 2000, yawan kudin taimako da Sin ta samarwa kasar Kamaru a fannin raya tattalin arziki ya kai cefa biliyan 3000. Ya yi imani da cewa, bayan kammala taron FOCAC na wannan karo akwai kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar Sin da Afirka

Jaridar Daily Graphic ta kasar Ghana ta labarto cewa, a matsayin ta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, Sin ta san muhimmancin dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa da kuma kasashen Afirka. Ana daukar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a matsayin hadin gwiwa ta samun moriyar juna, kuma ana raya ta ne a kokarin da ake na ganin an farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China