Xi Jinping: Kasashen Afirka suna bunkasa yadda ya kamata
A yau Jumma'a 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a bikin bude taron koli na Johannesburg na FOCAC cewa, yanzu nahiyar Afirka tana bunkasa yadda ya kamata, hakan ya farantar ma kowa. Ya lura da cewa, kasashen Afirka suna kokarin neman samun hanyar bunkasuwa da ya dace da su, kuma suna tsayawa tsayin daka kan daidaita batutuwa da kansu. Ban da haka, kasashen Afirka suna kokarin zamanintar da masana'antu, da neman samun dauwamammen ci gaba da kansu, shi ya sa suke samun ci gaba cikin sauri. Bugu da kari, shugaban na kasar Sin ya lura da cewa, kasashen Afirka suna kokarin samun ci gaba tare da juna, da zummar yin hadin kansu a yayin daidaita harkokin duniya.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku