Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming ya shaidawa taron manema labarai cewa, wadannan tanade-tanade za su taimaka wajen raya masana'antu da bangaren aikin gona na nahiyar.
Shi ma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa, za a yi baje kolin kayayyakin masana'natu a yayin taron dandalin, bikin da ake fatan zai ba da damar kulla harkokin kasuwanci a bangarorin jiragen kasa da na sama, wutar lantarki da harkokin sadarwa.
Ana kuma sa ran shugabannin siyasa da na masana'ntu za su yi amfani da wannan dama wajen yin musayar ra'ayoyi.
Kimanin shugabannin kasashe 36 da na gwammatoci 5 da mataimakan firaministoci 3 da shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ne za su halarci wannan taro mai tarihi, inda kasashe masu tasowa za su hadin kan da ke tsakaninsu. (Ibrahim Yaya)