Asusun na CAD ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba.
Wannan yana daya daga cikin matakai 8 da gwamnatin kasar Sin ta sanar a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC a shekarar 2006 da ya gudana a birnin Beijing.
Wannan mataki na nuna cewa, an kara yawan kudin da ake yi amfani a asusun CAD sau uku kafin bude taron kolin FOCAC na Johannesburg, lamarin da ke nuna cewa, zuba jari a nahiyar Afirka yana da matukar ma'ana ga hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, kana ya alamta cewa, asusun CAD yana bunkasa cikin sauri a harkokin dandalin zuba jari da tattara kudi na Sin da kasashen Afirka. Bayan da aka kammala samar da kudi ga asusun a karo 3, hakan zai kara karfin zuba jari ga Afirka, da nuna goyon baya ga kamfanonin Sin ta yadda za su raya ayyukansu a kasashen Afirka. (Zainab)