Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci hadin gwiwar kasashen Afirka, wajen bunkasa manufofin cimma moriyar juna da ci gaba tare, karkashin inuwar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka na FOCAC.
Shugaba Xi ya bayyana wannan bukata ne cikin jawabinsa, ga mujallar hadin gwiwar Sin da Afirka, game da muhimman batutuwan da za a tattauna yayin dandalin na FOCAC. Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin da Afirka na da makoma guda a fannin ci gaba.
Har wa yau shugaba Xi ya bayyana cewa, sassan biyu sun shafe tsahon lokaci tare, yayin da kuma a yanzu suke fuskantar wani yanayi na karuwar damammaki da hadin gwiwa mai ma'ana. Ya ce, Sin na matukar martaba, tare da goyon bayan ci gaban al'ummun nahiyar Afirka, matakin da ke da matukar tasiri ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban bil'adama baki daya.(Saminu)