A jiya ne aka bude taron 'yan kasuwa na kasashen Sin da Afirka karo na 5 a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu, inda asusun raya Sin da Afirka wato CAD ya daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da hukumar raya masana'antu ta MDD wato UNIDO, asusun Melinda Gates, asusun Africa 50 da kuma kungiyar 'yan kasuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin.
A jawabinsa yayin taron shugaban asusun CAD Chi Jianxin ya bayyana cewa, asusun CAD ya hada kai tare da hukumomin kasa da kasa ta yadda za a zuba jari a Afirka, tare da karfafa hadin gwiwa a Afirka, fadada yankunan zuba jari, da janyo karin kamfanonin Sin su kara zuba jari a nahiyar Afirka ta yadda za a gaggauta raya tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummomin kasashen Afirka. (Zainab)