Shugaban kasar Sin Xi Jinping a jawabin da ya gabatar wajen bikin bude taron koli na FOCAC da ake yi a birnin Johannersburg na Afrika ta Kudu a ranar Jumma'an nan 4 ga wata, ya tabbatar da cewa, Sin na fatan aiwatar da manyan shirye-shiryen hadin gwiwa 10 tare da Afrika a shekaru 3 masu zuwa don ingiza dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, wadannan shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika sun shafi fannoni 10.
A cewar shi wadannan fannoni sun hada da masana'antu, aikin gona na zamani, manyan ababen more rayuwa, hada-hadar kudi, raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Haka kuma ciki akwai bangaren ciniki da zuba jari, kawar da talauci da amfanawa jama'a, kiwon lafiya, al'adu da kuma shimfida zaman lafiya da tabbatar da tsaro. (Amina)