Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana aniyar kasarsa, ta hada kai da nahiyar Afirka, domin cimma nasarar hadin gwiwa, da kawance wanda zai amfani al'ummun sassan biyu.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin liyafar da aka shiryawa shugabanni mahalarta taron kolin dandalin FOCAC na bana wanda ke gudana a kasar Afirka ta Kudu. Ya kuma kara da cewa, Afirka nahiya ce da kasarsa ta amincewa kuma take girmamawa. Kaza lika ya bayyana nahiyar a matsayin yankin da ke cike da tarihi, da kyakkyawan fata na ci gaba.
Nahiyar Afirka ce yankin farko da shugaban na Sin ya fara ziyara, bayan zaman sa shugaban kasa a shekara ta 2013. Ya kuma taba bayyana ta a matsayin nahiya mai cike da ni'imomi da albarkatu.(Saminu)