Wannan shi ne karo na farko da kasashen Sin da Afirka za su shirya bikin baje koli na na'urori a Afirka tare.
Haka kuma, a yayin taron maneman labaran da aka yi a wannan rana, Qian Keming ya ce, wannan shi ne karo na farko da za a nuna manyan na'urorin da kasar Sin ta ke kerawa a nahiyar Afirka, wannan ya sa kasar Sin ta zabi wasu kamfanonin da suka shahara a fannonin da suka shafi layin dogo, jiragen sama, wutar lantarki, sadarwa da dai sauransu da su halarci bikin.
A halin yanzu kuma, kasar Sin na dukufa wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa game da gina kayayyakin more rayuwa da kuma ciyar da aikin masana'antu gaba, kuma yanzu haka kasashen Afirka na kokarin raya harkokin masana'antu, lamarin da ya sa burin neman bunkasuwa na Sin da Afirka ke dacewa da juna sosai. Don haka ana ganin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu na da makoma mai haske. (Maryam)