in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya tashi zuwa birnin Paris da Afrika
2015-11-29 12:49:12 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bar birnin Beijing a ranar Asabar domin wata ziyarar aiki a birnin Paris na kasar Faransa da kuma nahiyar Afrika.

Shugaba Xi zai halarci bikin bude dandalin sauyin yanayi na MDD karo na 21 a birnin Paris daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Nuwamba bisa goron gayyatar shugaban Faransa Francois Hollande da kuma ministan harkokin wajen kasar kuma shugaban wannan taro mista Laurent Fabius.

Haka kuma shugaba Xi zai kai ziyara a kasar Zimbabwe daga ranar 1 zuwa 2 ga watan Disamba bisa goron gayyatar shugaban kasar Robert Mugabe.

Daga nan kuma zai wuce zuwa kasar Afrika ta Kudu daga ranar 2 zuwa 5 ga watan Disamba bisa goron gayyatar shugaban kasar Jacob Zuma, inda zai shugabanci taron dandalin Sin da Afrika da za a shirya a birnin Johannesburg. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China