in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka ta Kudu sun lashi takwabin bunkasa hadin kai tsakaninsu
2015-12-03 09:13:42 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, sun tattauna kan yadda za su kara bunkasa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.

Bugu da kari shugabannin sun amince sun kara daga matsayin dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar shekaru 5-10 bisa manyan tsare-tsare da kasashen biyu suka cimma, inda za su jagoranci taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen biyu su kara karfafa bangarorin hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta hanyar mutunta juna, da samun moriya tare, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

A nasa jawabin, shugaba Zuma ya ce, kasarsa tana maraba da karin zuba jari daga bangaren kasar Sin. Yana kuma fatan sassan biyu za su kara yin hadin gwiwa a wasu fannonin kamar cinikayya, fasahar kere-kere, makamashi, harkokin kudi, kayayyakin jiragen ruwa, da harkokin jiragen sama.

Sauran fannonin sun hada da musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu, matakin da a cewar shugaba Zuma zai kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a kungiyoyin kasa da kasa, kamar MDD da kungiyar G20 da sauran manyan batutuwa na duniya kamar matsalar sauyin yanayi.

Har ila shugaba Zuma ya ce, yana goyon bayan kasar Sin na karbar bakuncin taron kolin G20 da za a gudanar a birnin Hangzhou da ke gabashin kasar Sin daga ranar 4-5 ga watan Satumban shekara mai zuwa.

Bayan tattaunawar, shugabannin sun kuma shaida sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, cinikayya, al'adu, kimiyya da fasahar kere-kere.

A ranar Jumma'a ne za a bude taron kolin dandalin FOCAC a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, inda ake sa ran tsara matakan zurfafa dangantaka tsakanin Sin da Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China