Jakada Lin ya ce, an canja taron ministoci karo na 6 na FOCAC da za a yi a birnin Johannesburg dake Afrika daga ranar 4 zuwa ranar 5 ga watan bana zuwa taron kolin FOCAC, haka kuma kasar Sin da ta Afrika ta Kudu za su shirya taron tare. Ana sa ran mambobin kasashen FOCAC 50 ne za su tura shugabanni ko kusoshin gwamnati don halartar taron, sannan shugabannin kungiyar AU ma za su halarci taron, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi muhimmin jawabi.
Ya ce, wannan shi ne karo na biyu da aka shirya taron kolin na FOCAC tun bayan kafuwarta shekaru 15 da suka gabata, kuma wannan shi ne karo na farko da aka shirya taron kolin FOCAC a nahiyar ta Afrika, kazalika, wannan shi ne karo na farko da Sin ta shirya babban bikin a kasashen waje.
Jakada Lin ya ce, ya zama dole bangarorin biyu su yi amfani da wannan dama, don inganta hadin gwiwa a fannin raya masana'antu, da aikin gona na zamani da kiwon lafiya, da musayar al'adu da samar da tsaro. Haka kuma, a yayin taron, kasar Sin za ta sanar da sabuwar manufa, da sabbin tunani ga kasashen Afrika, kana da wasu matakan inganta hadin gwiwa don cin moriyar juna a tsakaninsu.
Akwai bukatar hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, in ji jakadan.(Bako)