in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU
2015-12-03 17:22:30 cri

 

A yau Alhamis 3 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugabar hukumar zartaswar kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU), madam Nkosazana Clarice Dlamini-Zuma, a birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.

A yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya bayyana cewa Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kungiyar AU, ta na kuma goyon bayan kungiyar, wajen taka muhimmiyar rawa a fannin raya nahiyar Afirka, da samun ci gaba tare, da kuma daidaita harkokin shiyya shiyya da na duniya baki daya.

Shugaba Xi ya kara da cewa Sin tana tsayawa tsayin daka game da goyon bayan ta ga mutanen Afirka, wajen daidaita batutuwan nahiyar da kansu, ba kuma za ta sa hannu cikin harkokin gida na kasashen Afirka ba. Kaza lika Sin ta nuna goyon baya ga kokarin kungiyar AU, na tabbatar da zaman lafiya a nahiyar, tare da fatan karfafa hadin gwiwa a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro tsakaninta da kasashen na Afirka, da kara yin shawarwari kan muhimman batutuwan duniya, da kokarin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa a wurare daban daban.

A nata bangare, madam Zuma ta furta cewa, a daidai wannan lokaci na cika shekaru15 da kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, shugaba Xi ya ziyarci kasar Afirka ta Kudu, tare da ba da jagoranci ga taron koli karo na biyu, hakan na da ma'ana sosai. Daga nan sai ta gabatar da matukar godiya bisa taimakon da Sin ke baiwa nahiyar Afirka cikin dogon lokaci. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China