in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya ba da umurnin sanya wa Turkiyya takunkumi
2015-11-29 14:13:28 cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sa hannu kan umurnin sanya wa Turkiyya takunkumi a ran 28 ga wata, matakin da ya shafi hana kamfanonin yawon shakatawa da su gudanar da aikinsu a Turkiya. Ban da wannan kuma, umurnin ya nemi gwamnatin kasar da ta dauki matakin hana zirga-zirgar jiragen saman haya tsakanin Rasha da Turkiya, da sa ido kan ayyukan kamfanin sufurin Turkiyya dake kasar Rasha, da kuma sa ido kan tashoshin jiragen ruwa da ba da tabbaci kan tsaron sufurin jiragen ruwa a sararin tekun Azoz da na Black sea, matakan da za a dauka sun hada da hana jiragen ruwan kasar Turkiya da su tsaya ko ratsa sararin tekun Rasha. Ban da wannan kuma, an ce daga ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2016, ban da ma'aikatan diplomasiyya da iyalensu na kasar Turkiya da mutane dake da takardar wucin gadi ta shaidar iznin zauna a Rasha, sauran 'yan kasar Turkiya ba su iya shiga kasar Rasha ba.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Turkiya ta ba da wata sanarwa a ran 28 ga wata cewa, ta gano akwai 'yan kasarta da suka fuskanci matsaloli a lokacin da suke ziyara ko neman samun wurin zauna a kasar Rasha, hakan ya sa ta yi kira ga jama'arta da su dakatar da kai ziyara a Rasha.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan a jiya Asabar ya bayyana takaici game da harbo jirgin saman yaki na kasar Rasha da kasarsa ta yi, kuma ya yi kira ga shugaban Rasha da su gana da juna a birnin Paris a yayin taron sauyin yanayin duniya da za a bude. Wannan ya kasance karo na farko ne da Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana takaicinsa game da lamarin, kuma ya yi kira ga shugabannin kasashen biyu da su zauna a kan teburin shawarwari domin bullo da wata hanyar warware wannan matsala. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China