Wata hira da aka tara tsakanin mayakan kungiyar IS dake yankin Sinai, da kuma mambobin IS dake kasar Syria, ta tabbatar da sahihancin shelar da kungiyar ta yi na daukar alhakin kai harin jirgin saman Rasha, in ji gidan talabijin na CBS News, tare da ruwaito wasu majiyoyin kusa da masu leken asirin Amurka.
A cewar wadannan kafofin, Amurka ta tare wasu kalaman mayakan IS dake nuna cewa wani mutuminsu ya samu shiga filin jirgin saman Charm El-Cheikh, dake kudancin yankin Sinai na kasar Masar.
Yanzu Amurka na aiki tare da mutanen Rasha, bayan da Rashar ta nemi taimakon FBI, a cewar CBS News, tare da kara cewa Washington har yanzu bai raba wannan labari ba tare da Moscow.
Jirgin saman Airbus A321 dake bisa hanyarsa ta zuwa Rasha, ya fado a ranar 31 ga watan Oktoba a yankin Sinai bayan ya tashi daga filin jirgin saman Charm Al-Cheik, tare da halaka fasinjoji 224.
Jim kadan bayan hadarin, kungiyar IS ta sanar daukar alhakin aikata wannan dayen aiki a cikin wata sanarwa, tare da bayyana cewa ta yi hakan ne domin mayar da martani kan luguden wutar da jiragen yakin Rasha suke kaiwa kan kungiyar IS a Syria. (Maman Ada)