Wani kamfanin dillancin labarai mai zaman kansa ya ba da rahoton cewa, jirgin ya fado ne a tsaunukan Turkmen da ke yankin Kizidag a kudancin kasar Turkiya.
Gidan talabijin na al-Mayadeen da ke watsa shirye-shiryen cikin harshen Larabci a kasar Syria, ya ruwaito majiyoyin sojan kasar Turkiya na cewa, jirgin saman kasar Turkiya samfurin F-16s ne ya harbo jirgin Rasha, bayan ya yi masa gargadin cewa ya keta sararin samaniyar kasar.
A ranar Jumma'a ne dai ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta kira jakadan kasar Rasha da ke Ankara domin ta bayyana rashin jin dadinta kan hare-haren da Rashar ke kaddamarwa a kauyukan Turkmen da ke arewacin kasar Syria.
Gwamnatin Turkiya dai ta sha yi wa Rasha gargadi kan ta kawo karshen hare-haren da ta ke kaiwa a yankin. (Ibrahim)