Shugaba Putin wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da sarki Abdullah na Jordan na biyu a birnin Sochi na Rasha, ya ce Turkiya ta harbo jirgin nata ne kimanin kilomita 1 daga kan iyakar kasar, sannan ya fado a yankin da ya kai nisan kilomita 4 daga wurin da aka harbo shi.
Ya kuma tabbatar da cewa, jirgin da matukinsa ba su yi wata barazana ga Turkiya ba. Don haka ya ce, wannan lamari tamkar cin fuska ne. (Ibrahim Yaya)