in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu jiragen saman yaki na Rasha sun kaddamar da hare-hare a Palmyra
2015-11-09 10:09:36 cri
Wasu jiragen saman yaki na kasar Rasha, sun kaddamar da hare-hare kan mayakan kungiyar IS a birnin Palmyra dake kasar Sham.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar mutum guda tare da jikkatar wasu da dama, sakamakon hare-haren na ranar Lahadi. Tun dai cikin watan Satumbar da ya gabata ne Rasha ta fara kaddamar da hari ta sama kan sansanonin kungiyar ta IS a kasar ta Sham.

Ko da yake gwamnatin Sham na jinjinawa wannan aiki da Rasha ke gudanarwa, a hannu guda 'yan adawar kasar na cewa hakan wani mataki ne kawai na tallafawa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

A nata bangare Rasha na cewa babban burin ta shi ne taimakawa duk wani shiri da zai kai ga warware rikicin siyasar kasar ta Sham cikin ruwan sanyi.

A ranar 20 ga watan Mayun da ya gabata ne dai mayakan IS suka amshe ikon garin Palmyra, daga nan ne kuma suka fara lalata muhimman wuraren tarihi, da suka hada da kaburbura, da ma gidajen yarin soji dake birnin. Kaza lika 'yan kungiyar ta IS sun rika hallaka sojojin gwamnati, da ma sauran mutanen da suke zargi da taimakawa mahukuntan kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China