Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry dake ziyara a yankin tsakiyar Asiya ya shaidawa manema labaru a jiya Litinin cewa, kasashen yamma za su soke takunkumin da suka kakkabawa kasar Rasha bayan da aka aiwatar da sabuwar yarjejeniyar Minsk.
John Kerry ya ce, a cikin sabuwar yarjejeniyar Minsk, an bukaci dakarun dake gabashin kasar Ukraine da gwamnatin kasar su dauki wasu matakai, hakan yana da muhimmanci sosai ga aikin gudanar da sabuwar yarjejeniyar Minsk. Ya kuma kara da cewa, ba za a nuna sassauci kan batun Ukraine ba, kasashen yamma za su soke takunkumin da suka kakabawa kasar Rasha bayan da aka gudanar da sabuwar yarjejeniyar Minsk, kana za a farfado da hulda a tsakanin kasashe yamma da kasar Rasha yadda ya kamata.(Lami)