Wannan shi ne sabon matakin da kasar Rasha ta dauka domin kasar Turkiya ta ki neman gafara daga wajenta bayan da ta harbo wani jirgin saman yaki na kasar Rasha a sama wanda ke kan iyakar dake tsakanin Turkiya da Syria. Haka kuma, gwamnatin kasar Rasha ta bada shawara ga jama'ar kasar da kada su yi yawon shakatawa a kasar Turkiya.
Ban da haka kuma, Mr. Lavrov ya bayyana a yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Syria, Walid Muallem cewa, bisa gayyatar da kasar Syria ta yi mata, kasar Rasha za ta ci gaba da taimaka ma kasar kamar yadda take bukata, har sai an kai ga hallaka 'yan ta'adda baki daya.
Dangane da batun harbo jirgin saman yakin kasar Rasha da kasar Turkiya ta yi kuma, Mr.Lavrov ya ce, kasar Turkiya ta riga ta kure hakurin kasar Rasha, kuma ta shigar da kanta zuwa wani mawuyacin hali ba kawai ga moriyar kasar ba, har ma kuma ga yanayin yankin baki daya. (Maryam)