Shugaba Putin ya bayyana hakan ne jiya Alhamis a fadar Kremlin, yayin da yake zantawa da manema labaru tare da takwaransa na kasar Faransa François Hollande, wanda ke ziyara a kasar ta Rasha.
Ya ce, bayan kasashen biyu sun gudanar da shawarwari, za su fara hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu da hadin gwiwa a tsakaninsu da kawancen kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka. Ya kuma jaddada cewa Rasha na mutunta wannan kawance.
A cewar sa, ya fi kyau a kafa wata kawancen na kasashen duniya bai daya, hakan zai sa kaimi ga gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci mai amfani, sai dai a daya hannun ya nuna rashin amincewa da harbo jirgin saman yakin Rasha, da ma mutuwar sojojin Rashan.
A nasa bangare kuwa, shugaba Hollande cewa ya yi, bisa shawarwarin da ya yi tare da Putin, za su shiga ayyukan murkushe 'yan ta'adda na kungiyar IS a Siriya kawai, amma ba dakarun dake yaki da 'yan ta'adda ba. Ya ce, Rasha da Faransa za su yi musayar bayanai game da hakan, don tabbatar da wadanda za a yaka.(Bako)