Shugaban Putin ya gana da ministan sufurin kasar Maksim Sokolov wanda tuni ya ziyarci wurin da hadarin ya auku, Putin ya bayyana hadarin a matsayin wata babbar masifa ce. Sannan ya jaddada bukatar a ci gaba da bincike, kuma ya bukaci jami'ai masu bincike da su yi taka tsan-tsan game da hare-haren ta'addanci a wannan yanki.
A bangare guda kuma, sakatare janar ga shugaban kasar Rasha game da yada labaru Dmitri Peskov ya ce, kasancewar yanzu ne, aka fara gudanar da bincike, ba zai yiwu a bayyana dalilan da suka haddasa hadarin ba.
Bisa labarin da aka samu, an ce, tuni an riga an samu bakaken akwatuna 2 na jirgin, kuma tuni kwararru daga kasashen Rasha da Faransa da Jamus da na kamfanin Airbus suka fara binciken musabbabin hadarin jirgin.(Bako)